TCN Zata Samar Da Mitoci Miliyan Hudu Masu Amfani Wutar Lantarki A Fadin Najeriya

0 206

Hukumar kula da wutar lantarki ta kasa ta ce nan ba da dadewa ba za ta samar da mitoci miliyan hudu ga masu amfani da wutar lantarki a kasar.

Kwamishiniyar hukumar mai kula da harkokin kwastomomi, Aisha Mahmud, ta bayyana hakan a wajen taron warware korafe-korafen kwastomomin wanda aka shirya jiya a Jos, jihar Filato.

Aisha Mahmud, ta bayyana karancin mitoci a kasar nan a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin da hukumar ke fuskanta a halin yanzu, inda ta yi nuni da cewa nan ba da dadewa ba kalubalen zai zama tarihi.

Ta ce an samar da hanyoyin samar da mitoci ta hanyar shirin samar da mitoci masu dimbin yawa na gwamnatin tarayya.

Aisha Mahmud, ta ce an kammala dukkan shirye-shiryen samar da mitocin, inda ta bayyana cewa babban bankin kasa CBN ne zai dauki nauyin shirin. Aisha Mahmud ta kuma danganta karuwar farashin wutar lantarki da hauhawar farashin kayayyaki, da karyewar darajar Naira, da tsadar iskar gas, da samar da aikin yi, da sauran abubuwan da suka shafi tattalin arziki a kasar nan.

Leave a Reply