Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kare matakin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta ɗauka, inda ya ce ya yi haka ne domin ƙasar ta samu ci gaba.
Shugaban ya bayyana haka ne ranar Juma’a a fadarsa da ke Abuja, lokacin da yake karɓar bakuncin jakada na musamman daga ƙasar Qatar, Dakta Mohammed bin Abdulaziz Al-Khulaifi.
Tinubu ya ce tsare-tsare da ake ɗauka na inganta harkar haraji a Najeriya, ya sa mutane daga ƙasashen waje na samun saukin zuba-jari da kuma kasuwanci a ƙasar.
“Muna ƙoƙari don inganta tsarin harajin mu. Wajibi ne mu ɓullo da sabbin tsare-tsare idan muka duba abubuwan da suka faru a baya na wahalhalu da aka fuskanta.
“Na ɗauki matakai masu tsauri saboda mu samu ci gaba. Sannu a hankali kwalliya za ta biya kuɗin sabulu,” in ji shugaban.
Ya ce za a inganta haɗin-kai tsakanin Najeriya da Qatar ne ta hanyar duba batun wadatar abinci da kuma ci gaban tattalin arziki.
“Ba za ka samu abokin hulɗa fiye da Najeriya ba. Na kasance ina bibiyar abubuwan da ke faruwa a duniya da kuma ƙoƙarinku. Ya kamata ku ƙara himma a Najeriya don yaƙi da talauci da kuma ayyuka jin-ƙai,” kamar yadda Tinubu ya faɗa wa jakadan na ƙasar Qatar.