Tinubu ya amince da ƙarawa Babban Sefotun ‘yan sandan Kayode Egbetokun wa’adin shekara 3

0 76

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarawa Babban Sefotun ‘yan sandan Kayode Egbetokun shekaru 3, kamar yadda wata majiya daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta bayyana.

An ƙara wa shugaban ‘yan sandan wa’adin shekara uku ne, ma’ana sai zuwa 2027.

Ta ruwaito cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ne ya bai wa Babbab Sufeton ‘yan sandan takartar ƙara masa wa’adin a yiwa Litinin.

A watan Yulin da ya gabata ne Majalisar Dattijai ta yi garambawul ga dokar ‘yan sanda ta 2020 ƙarƙashin sashe na 8, wadda ta ci karo da ƙarawa ma’aikacin gwamnati wa’adin aiki bayan shekaru 35 ko kuma bayan kaiwa shekaru 60.

Egbetokun wanda aka naɗa a watan Yunin 2023 zai cika shekaru 60 ne a gobe laraba 4 ga watan Satumba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: