Shugaban ya kuma amince da dakatar da biyan riba da aka samu a 2024 ga gwamnati don taimakawa da kuɗaɗen da kamfanin zai kashe.
Idan ba’a manta ba a ranar 29 ga watan mayun 2023 shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur sai dai akwai alamun da ke nuna cewar har yanzu gwamnati na kashe kuɗaɗe masu yawa a kan tallafin.
Wannan na biyo bayan zanga-zangar tsadar rayuwa da yan najeriya sukayi a ƙasar,wanda ɗaya daga cikin buƙatunsu shi ne a dawo da tallafin man fetur din.
Amma a cikin wani jawabin da Tinubu ya yi, ya bayyana cewa dawo da tallafin man fetur ba zai yiwu ba, inda ya bayyana cire tallafin a matsayin abu mai wahala amma kuma wajibi ne gwamnatinsa ta yi.
Ya ce tallafin ya kasance tamkar wata sarƙa da ta ɗaure tattalin arziƙin na Najeriya.
A ranar Litinin, wata jarida a Intanet ta ruwaito cewa Tinubu ya amince wa NNPCL da ya biya tallafin bayan da kamfanin ya koka cewa ya yi amfani da duk hanyoyin da zai iya don samar da isasshen man fetur a ƙasar nan amma hakan ya gagara.
NNPCL ta shaida wa shugaban cewa waɗannan ƙoƙarin sungaza warware matsalar da ake fuskanta, kuma idan ba a biya tallafin ba, kamfanin ba zai iya sanya kuɗin da ake buƙata daga gare shi ga asusun Gwamnatin Tarayya ba.
Don haka, Tinubu ya umarci kamfanin da ya yi amfani da haraji da sauran kuɗaɗen da aka ware wa Gwamnatin Tarayya domin biyan kuɗaɗen tallafin man fetur.