Tinubu yace yawan jama’ar Najeriya da ke ƙaruwa cikin sauri na buƙatar ingantattun matakan masana’antu

0 527

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yawan jama’ar Najeriya da ke ƙaruwa cikin sauri na buƙatar ingantattun matakan masana’antu domin mayar da wannan dama ta zama riba.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a lokacin bikin taron  zuba hannayen jari na Taraba (Taravest) da aka gudanar a birnin Jalingo, babban birnin jihar Taraba, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilce shi.

Tinubu ya ce Najeriya ba za ta ci gaba da dogaro da albarkatun ƙasa marasa sarrafawa ba, inda ya jaddada buƙatar kafa masana’antu da za su ƙara darajar kayayyaki, tare da hade-haden kirkire-kirkire da wuraren masana’antu na zamani da za su sauya dabaru zuwa aiki mai tasiri.

A cewarsa, la’akari da hasashen cewa Najeriya za ta zama ƙasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya nan da shekarar 2050, wannan hauhawar yawan jama’a na iya zama barazana ga ci gaban ƙasa muddin ba a tsara yadda za a amfana da shi ba.

Shugaban ya ce akwai babbar dama ta amfani da matasa masu ƙwazo da kuzari da Najeriya ke da su, musamman ganin yadda ake fama da ƙarancin ƙwararrun ma’aikata a duniya.

Ya ƙara da cewa taron zuba jari na Taraba yana da matuƙar muhimmanci, domin jihar na da damar ba da gudunmawa mai ma’ana ga cigaban ƙasa fiye da kyawawan tsaunukanta da sauran abubuwan yawon buɗe ido.

Tinubu ya bayyana cewa duniya na cikin sabon salo na juyin juya halin masana’antu, wanda hakan na nufin dole ne Najeriya ta ƙara yawan masana’antunta da ingancin samar da kaya domin daidaitawa da yawan jama’ar ƙasar.

Leave a Reply