Tinubu yana farin ciki kan yadda ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC

0 140

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan yadda ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa ke ci gaba da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Ya kuma buƙaci shugabancin jam’iyyar da su ci gaba da karɓar sababbin mambobi domin ƙarfafa jam’iyyar.

Tinubu ya bayyana haka ne a taron ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a jiya a dakin taro na Banquet Hall na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda jam’iyyar ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Tinubu a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a 2027.

Gwamnoni 22 na APC da shugabannin majalisar dokoki ta ƙasa sun bayyana goyon bayansu ga Tinubu, tare da bayyana cewa ba su da wani ɗan takara face shi.

Shugaba Tinubu ya yi watsi da zargin da ake masa na ƙoƙarin kafa jam’iyya ɗaya a ƙasar, yana mai cewa ba laifin APC bane idan ’yan siyasa suna barin jam’iyyun da suka kira “jirgi mai lunkuwa.”

Tun da farko, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya amince da Tinubu a matsayin ɗan takara guda ɗaya na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Leave a Reply