Trump ya sanar da cewa zai ninka harajin ƙarafa da Samfolo zuwa kashi hamsin a ranar Larabar wannan makon

0 346

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa zai ninka harajin ƙarafa da Samfolo zuwa kashi hamsin a ranar Larabar wannan makon, domin kare waɗannan sassa biyu na Amurka.

Ya bayyana hakan ne a wani taro da aka yi a wani kamfanin sarrafa ƙarafa na Amurka da ke Pennsylvania, inda ya kuma sha alwashin dakatar da duk wata ƙasa da ta nemi yin bara’a ga sabon matakin.

Ya ce idan ƙasa ba ta da ƙarafa, ba ta cika ƙasa ba, ba za ta iya samar da makamai ba, don haka zai zamana ba ta da wani zaɓi illa zuwa ga China don neman taimakon makamai da jiragen ruwa da sauran abubuwan da ake samarwa da ƙarafa. A makon da ya gabata ne wata kotu a Amurkar ta yanke hukuncin cewa harajin da ya saka kan kayayyakin da ake shigo da su daga ƙetare ya saɓa wa doka, ko da yake an dawo da shi na wucin gadin bayan ɗaukaka ƙara

Leave a Reply