Tsohon Dan Majalisar Jihar Yobe Hon Audu Babale, ya yi sauyin sheka shida dubban Magoya bayan sa zuwa Jam’iyar APC a birnin Damaturu na Jihar.

Hon Babale ya taba zama Dan Majalisar mai wakiltar Goya/Ngeji a karamar hukumar Fika ta Jihar.

Cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Hussaini Mai Suleh ya rabawa manema labarai ya ce mai sauyin shekar ya ce ya gamsu da shugabancin Gwamna Mai Mala Buni na Jihar.

Sanarwar ta ce Mataimakin Gwamnan Jiha Alhaji Idi Barde Gubana, shine ya karbi mai sauyin shekar a madadin gwamna, inda ya bashi tabbacin daukar sa tamkar kowanne dan Jam’iya.

Kazalika Idi Barde Gubana ya ce gwamna Mai Mala Buni, ya na kallon duk wanda ya yi sauyin sheka zuwa jam’iyar APC a matsayin cikakken yan Jam’iya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: