Tsohon gwamnan CBN Sanusi Lamido ya ce wasu mutane a Najeriya na yin amfani da addini domin su rufe gaskiyar al’amura

0 66

Tsohon gwamnan babban bankin kasa CBN, Sanusi Lamido Sanusi, ya ce wasu mutane a kasarnan na yin amfani da addini domin su rufe gaskiyar al’amura.

Ya yi wannan jawabi ne a jiya lahadi, a wurin taron kasa karo na 5 na kungiyar maza musulmi masu sana’a da aka gudanar a babban dakin taro na J.F, Ade-Ajayi na Jami’ar jihar Legas.

Ya ce amincewa da bankunan da ba ruwansu da ruwa a kasar nan ya kawo cigaba a kasar nan tare da cire shakku a zukatan wadanda ba musulmai ba.

Sanusi ya kara da cewa Tsarin kudin, ya haifar da cece-kuce a tsakanin addinai.

Amma, wandanda ba musulmi ba, daga baya sun rungumi shi saboda alfanun da ke tattare da shi domin kashi 40 cikin 100 na wadanda suka fara karbar hannun jarin bankin Jaiz ba musulmi ba ne.

Sanusi ya ce babu dalilin da zai sa Najeriya ba za ta iya zama cibiyar bankin Musulunci a Afirka ba.

Anasa  bangaren Babban bako mai jawabi a wurin taron, Farfesa AbdulRazzaq Alaro ya karyata ra’ayin cewa bankin Musulunci yana da manufar Musuluntar da yan Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: