Tsohon Gwamnan Jigawa zai ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa a Abuja – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, na shirin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai taken Being True to Myself a Abuja ranar Talata, 13 ga watan Mayu, wanda ke ɗauke da muhimman bayanai kan tarihin siyasar Najeriya.
Shugaban kwamitin shirya taron, Sanata Mustapha Khabeeb, ya ce littafin na bayyana cikakken tarihi daga ƙarshen mulkin farar hula zuwa mulkin soja da yadda aka kafa jamhuriya ta huɗu, da kuma rawar da Lamido ya taka a matsayin Ministan Harkokin Waje a mulkin Obasanjo.
A cewarsa, littafin ba wai labarin mutum ɗaya bane kawai, illa wata taska da ke bayani kan haɗin kai, da amana, da yaƙin neman iko da ya shafi ci gaban demokaraɗiyyar Najeriya.
Sanata Khabeeb ya ƙara da cewa Lamido ya tsaya kan aƙidarsa duk da ƙalubale da shari’o’i da suka shafe shekaru, inda kotu ta wanke shi da ‘ya’yansa daga duk wata tuhuma da aka yi musu daga baya.