Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Birgediya Ibrahim Aliyu ya rasu

0 80

Marigayi tsohon gwamnan Jigawa, Ibrahim Aliyu, kafin rasuwarsa a jiya yana da mukamin Birgediya Janaral mai ritaya.

An haife shi a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 1947 a garin Yimirshika cikin karamar hukumar Hawul ta Jihar Borno.

Ya halarci makarantar firamare ta Yimirshika sannan ya wuce zuwa Provisional Secondary School, Maiduguri. Bayan kammala sakandire, ya wuce zuwa Nigerian Defence Academy Kaduna a shekarar 1968.

Ya zamo gwamnan jahar Jigawa na uku, sannan kuma na biyu a gwamnonin soja a shekarar 1993, inda ya gaji Alhaji Ali Sa’adu BirninKudu, bayan rugujewar gwamnatin rikon kwarya ta shugaban kasa Ernest Shonekan.

Ibrahim Aliyu ya yi gwamnatinsa a karkashin mukkin shugaban kasa Janar Sani Abacha.

Ya bar kujerar gwamnan Jihar Jigawa a watan Augustan shekarar 1996 inda Kanal Rasheed Shekoni ya gaje shi.

A lokacin mulkinsa, Ibrahim Aliyu ya nada Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr. Nuhu Muhammad Sanusi, a ranar 13 ga watan Janairun 1996.

Leave a Reply

%d bloggers like this: