Tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa bai da wata niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya bayyana cewa bai da wata niyyar tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekara ta 2027, kuma ba zai tsaya takara da Shugaba Bola Tinubu ba.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da daraktan yada labaransa, Michael Ohiare, ya fitar, inda ya karyata wani faifen bidiyo da ya sake bayyana a kafafen sada zumunta, wanda ke nuna cewa Bello ya fara kamfen domin kalubalantar Tinubu a 2027.
Ohiare ya bayyana bidiyon a matsayin ƙarya da ƙage da wasu masu neman tayar da zaune tsaye suka kirkira domin yaudarar ‘yan Najeriya.
Ya kara da cewa waɗanda ke ƙoƙarin ɓata sunan Yahaya Bello sun dade suna ƙirƙirar labaran ƙarya da nufin ɓata masa suna, amma ba su taba samun nasara ba. Sanarwar ta kuma ce wannan ba shi ne karo na farko da waɗannan mutane ke ƙoƙarin haddasa rikici tsakanin tsohon gwamnan da Shugaba Tinubu ba.