Labarai

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya sake sakin fursunoni 59 masu kananan laifuka a gidajen gyaran halin Kurmawa da Gorondutse a jihar Kano

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya saki fursunoni 59 masu kananan laifuka a gidajen gyaran halin Kurmawa da Gorondutse a jihar Kano.

Sarkin ya biya tarar Naira miliyan 17 ta cikin gidauniyarsa mai suna Muhammad Sanusi II.

Ko’odinetan gidauniyar Mujitaba Abba ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai jiya a Kano.

Ya bayyana cewa wanda ya kafa gidauniyar, Khalifa Muhammadu Sanusi llI kuma tsohon Sarkin Kano, ya bayar da izinin sakin fursunonin 59 bayan an biya tarar

Abba ya bayyana cewa a gidan yari na Kurmawa, sarkin ya biya tarar fursunoni 26, wanda ya kai Naira miliyan 4, da dubu 466 da 500.

Ya kara da cewa a gidan gyaran hali na Gorondutse, fursunoni 33 ne aka sako bayan an biya tarar kudi Niara milyan 11, da dubu 380, da 770.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: