Tsohon Shugaban kasa na rikon kwarya, Cif Earnest Shonekan, ya rasu.

Ya rasu ne a yau Talata a Legas yana da shekara 85 da hauhuwa a duniya.

Marigayin dai ya shugabanci Najeriya ne a matsayin Shugaban Kasa na rikon kwarya tsakanin ranar 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993

An kuma bashi rikon kwaryar kasar nan ne bayan shugaban mulkin soja na wancan lokacin Ibrahim Badamasi Babangida ya rusa zaben 12 ga watan Yuli na 1993.

Hakanne yasa aka bashi kasar domin kawo sasanto da kwanciyar hankali a wancan lokacin.

Tsohon Shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha ne ya hambarar da gwamnatinsa yayin wani juyin mulki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: