Gwamnatin tarayya ta karbi ƴan Najeriya kimanin 103 da aka koro daga kasar Turkiyya bisa wasu dalilai da suka shafi bakin haure da suka hada da ƙarewar wa’adin biza da shiga ƙasar ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu. Alhaji Tijani Ahmed, kwamishinan hukumar kula da ƴan gudun hijira da bakin haure ta kasa (NCFRMI) ne ya bayyana haka a yammacin jiya Juma’a, a lokacin da ake tantance waɗanda aka koro din a Abuja. Ahmed, wanda Amb. Catherine Udida, darakta mai kula da al’amuran hijira a hukumar ya wakilta, ya ce hukumar ta yi tsammanin za a aiko mutane 110 amma sai ta karbi 103, dukkansu maza. “Wasu daga cikinsu sun shafe wasu watanni a sansanin waɗanda aka koro, kuma yanzu da suke nan, muna fatan za mu bi diddigin duk wasu zarge-zargen da aka rubuta a kundin bayanansu. “Za mu bi ta fom din tantancewa, saboda wasu sun ce an kwace fasfo dinsu.”Za mu bi diddigin hukumomin Turkiyya, saboda har yanzu fasfo mallakin Tarayyar Najeriya ne,” in ji shi.