Tururuwar ƴan bindiga sun kashe ɗan majalisar jihar Kaduna Rilwanu Gadagau

0 157

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa ƴan bindiga sun kashe Rilwanu Gadagau wanda shi ne ɗan majalisar jihar mai wakiltar Giwa Ta Yamma.

Wasu makusantansa sun shaida wa BBC cewa maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne tun a ranar Litinin da dare a lokacin da ƴan bindiga suka kai hari a kan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Rahotanni sun ce an ga gawar ɗan majalisar ne a cikin daji a safiyar Laraba.

A ranar Talata ne dai aka samu rahoton cewa ƴan bindigar sun kai hari kan hanyar Kaduna zuwa Zaria inda aka tabbatar da mutuwar mutum ɗaya da sace mutane da dama.

Sai dai mun tuntuɓi rundunar yan sandan jihar Kaduna domin ƙarin bayani ba su ɗaga waya ba.

Asalin rahoton: BBCHausa

Leave a Reply

%d bloggers like this: