Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bayyana goyon bayanta ga mata masu neman tsayawa takara a zaben 2023

0 72

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, jiya a Abuja, ta bayyana goyon bayanta ga mata masu neman tsayawa takara a zaben 2023.

Aisha Buhari ta bayyana hakan ne a lokacin da ta ziyarci Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Bayan ganawar sirri da Abdullahi Adamu, uwargidan shugaban kasar ta shaidawa manema labarai cewa sun kai ziyarar ne domin taya shugaban jam’iyyar APC murnar wannan kyakkyawan aiki da yake yi wa jam’iyyar.

Tun da farko, ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta jaddada cewa kada a manta da mata a tsare-tsaren shirin jam’iyyar.

Hakan, a cewarta, ana samun mata a dukkanin mukamai a fadin duniya.

A tare da uwargidan shugaban kasa, akwai matar mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, da wasu manyan mata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: