Dahiru Buba, mutumin da ya shafe kwana 15 yana tafiya a ƙasa daga jihar Gombe zuwa Babban Birnin Tarayya, Abuja don murnar lashe zaɓe da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi a 2015 ya kamu da ciwon gaɓɓai.

Ya kamu da ciwon gaɓɓai mai tsanani, kuma a halin yanzu yana neman taimako, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

Mutumin, wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Dukku ne dake jihar Gombe, ya ce tattakin da ya yi a lokacin da Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe yake Sakataren Jam’iyyar na Ƙasa ba ta taɓuka masa komai ba sai takardar shaida.

Ya yi kira ga Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da su kawo masa tallafi.

“Tun lokacin da na yi tattakin, ciwon gaɓɓan yake ƙaruwa kullum.

“Ina kira ga Gwamnana, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe da shugabancin jam’iyya da su taimake ni in je asibiti”, in ji Mista Buba.

Mista Buba ya yi nuni da yadda rayuwa ta yi masa ƙunci saboda yadda ciwon gaɓɓan yake ƙaruwa, yana mai cewa ko kuɗin makarantar ‘ya’yansa ba ya iya biya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: