Wani ɗalibi makaho ya ɗauko wani makaho ɗan uwansa domin ya yi masa jarrabawar JAMB

0 185

Hukumar zana jarrabawar share fagen shiga manyan makarantu JAMB ta bayyana cewa wani ɗalibi makaho ya ɗauko wani makaho ɗan uwansa domin ya yi masa jarrabawa a madadinsa.

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce duk da kokarin hukumar wajen tallafawa masu buƙata ta musamman ciki har da mayar musu da kuɗin rajista da tanadin sufuri da masauki, hakan bai hana wasu aikata laifi ba.

A bana, ɗalibai 501 masu buƙata ta musamman ne suka zauna jarrabawar UTME a wurare 11 a fadin ƙasar nan, sai dai an kama ɗaya daga cikinsu da laifin amfani da mai kama da shi domin zana masa jarrabawar.

Hukumar ta nayyana cewa, sakamakon jarrabawar da aka fitar ya nuna cewa sama da ɗalibai miliyan ɗaya da rabi sun kasa samun makin 200, abin da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya danganta da nasarar yaki da maguɗi a yayain zana jarrabawar.

Leave a Reply