Wani abin fashewa ya tashi a wani ajin ɗalibai da ke nazarin tattalin arziƙi a Jami’ar Buea dake Kasar Kamaru

0 159

Wani abin fashewa da ya tashi a wani ajin ɗalibai da ke nazarin tattalin arziƙi a Jami’ar Buea dake kudu maso yammacin Kasar Kamaru ya jikkata mutane 11

A cewar wani malamin jami’ar Farfesa Ngomo Horace Manga, fashewar ta faru ne da yammaci bayan wani taron zaman lafiya, inda ɗalibai 11 suka ji raunuka, lamarin ya farune da misalin karfe 3:30 na yammacin jiya.

Farfesa Manga ya ce ba a samu wanda ya rasu ba cikin wannan lamari, kuma ɗaliban da suka jikkata samun kulawa a wani asibitin kuɗi da ke garin Buea.

Makarantu da dama sun ƙone a shekarun da suka gabata kuma ƙananan yara ba sa zuwa makaranta tun a shekara 2017.

Ƙungiyoyin ‘yan a-ware zuwa yanzu ba su yi iƙirarin kai wannan hari ba.

Kawo yanzu dai babu wata kungiyyar data dauki alhakin kai wannan hari.

Kawo yanzu dai babu wata kungiyyar data dauki alhakin kai wannan hari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: