Wani bam fashe ya kashe Sojoji 5 wanda suke aikin sintiri a Arewacin kasar Burkina Faso

0 75

Wani abun fashe ya kashe Sojoji 5 wanda suke aikin sintiri a Arewacin Burkina Faso, a cewar wata sanarwa da Sojin suka fitar a jiya.

Cikin wata sanarwa Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na Rana, a kusa da garin Mentao, inda Bom din ya fashe a cikin wata Mota.

Sanarwar ta ce kimanin Sojoji 5 ne suka mutu a sanadiyar fashewar Bom din yayin da kuma wani Soja 1 ya samu rauni.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu ikirarin Jihadi suke cigaba da kaiwa hare-hare a yankin tun daga shekara 2015.

Fiye da mutane dubu 1,500 ne hare-haren ya kashe, tare da tirsasawa mutane Miliyan 1 da dubu 400 barin muhallansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: