Wani fada da ya barke tsakanin mayakan Boko Haram da ke biyayya ga tsohon jagoran kungiyar Abubakar Shekau da kuma mayakan kungiyar ISWAP, wanda ya hallaka adadi mai yawa na ‘yan ta’addan ciki har da kwamanda guda da aka fi sani da Kundu.

Wasu majiyoyin tsaro sun ce a jiya alhamis ne fadan ya barke tsakanin bangarorin ‘yan ta’addan biyu a kananan hukumomin Dikwa da Bama inda har zuwa yanzu ba a samu cikakken alkaluman wadanda wannan fada ya hallaka ba.

Majiyar tsaron da ke tabbatar da batun ga manema labarai ta ce tun farko kwamandan kungiyar Boko Haram da ake kira Kundu ne ya kwaso wata zugar mayaka da nufin aikata fashi a kauyukan kananan hukumomin biyu, dalilin da ya sanya mayakan ISWAP kokarin dakatar da su.

Masanin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama ya ce yayin fadan na jiya ISWAP ta kashe gomman mayakan Boko Haram, ko da ya ke mambobinta da dama sun jikkata.

A cewar masanin tsaron, bayan shafe tsawon sa’o’i ana gwabza fadan tsakanin bangarorin ‘yan ta’addan biyu, da dama daga cikin mayakan Boko Haram sun gudu sun bar ababen hawansu tare da gawarwakin ‘yan uwansu da ISWAP ta kashe.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: