Wani Gidan marayu a Abuja sun bayyana yadda wasu yan Najeriya suke bayar da kayan abinci marar inganci ko kuma wanda lokacin lalacewarsu yayi ga marayu

0 28

Wani Gidan marayu a binin tarayya Abuja sun bayyana yadda wasu yan najeriya suke bayar da kayan abinci marar inganci ko kuma wanda lokacin lalacewarsu yayi ga marayu.

Da take jawabi yayin karbar kayan abinci daga kungiyar matan jami’an hakumar kashe gobara yau lahdi, shugaban marayun misis Blessing Ijenwa, ta koka da yadda wasu yaran suka kamu da rashin lafiya bayan cin gurbataccen abincin.

Tace basu zaci mutane zasu bayar da gurbataccen abinci ga marayu ba, kamar yadda suke samu a mafi yawancin lokuta yayin hadawa da cin abincin.

Haka kuma ta yabawa Hakumar FOWA bisa bayar da ingantaccen abinci ga marayun.

kazalika ta roki mutane dasu dinga kai ziyara gidajen marayu akai-akai domin nuna kulawa da sanin halin da suke ciki.

An rawaito cewa kungiyar FOWA ta bayar da buhunan shinkafa, da katon-katon na taliya da flawa, sabulai da man girki da dai sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: