Wani gini ya kama da wuta bayan fashewar wani abu a Legas

0 84

Kamar yadda BBC ta wallafa, “wani gini da ke kan titin Adeola Odeku a yankin Victoria Island na jihar Legas ya kama da wuta.

Gobarar ta tashi ne sakamakon wani injin janareto da ya kama da wuta da safiyar ranar Talata.

Wani shaida ya fada wa Jaridar The Cable a Najeriya cewa wata motar fasinja dauke da mutum uku ta kama da wutar bayan da ta tsaya a gefen ginin da ke ci da wutar.

Wutar ta shafi ababen hawa da wasu gine-ginen da ke kusa da inda lamarin ya faru.

Yayin da ya ke tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Legas LASEMA Nosa Okunbor, ya ce jami’an su na wajen da wutar ta kama domin kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: