Wani Hadarin Mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 5 a karamar hukumar Taura ta nan Jihar Jigawa

0 108

Wani Hadarin Mota yayi sanadiyar mutuwar mutane 5, yayin da wasu kuma suka samu raunika a karamar hukumar Taura ta nan Jihar Jigawa.

Kakakin Hukumar Tsaro na Farin Kaya wato Civil Defence CSC Adamu Shehu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai.

A cewarsa, hadarin ya faru ne a tsakanin wata Motar Golf, mallakin Alhaji Kabiru Muhammad mai shekaru 55 wanda ya fito daga Gujungu da kuma wata Motar Golf mallakin Kailua Saudi dan kyauyen Kiri mai shekaru 45 wanda ya fito daga Kano zuwa Gujungu.

Sanarwar ta ce hadarin de ya faru ne a kyauyen Nomi na karamar hukumar Taura, bayan sun yi taho mu gama, wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar mutane 5 ciki harda wani mai shekara 60 mai suna Malam Sallau da kuma Zulyadaini Muhammad mai shekaru 65, sauran mutane 3 ba’a iya gano sunayen su ba.

Kakakin Hukumar ta Civil Defence, ya ce gawarwakin mutanen da suka mutun suna dakunan Ajiye gawarwaki na Asibitin Ringim, sauran mutanen kuma da suka samu raunika suna cigaba da samun kulawar likitoci a Asibitin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: