Wani magidanci a jihar Abia, ya cinna wa kansa, matarsa da ƴaƴansa uku wuta bisa zargin matarsa Amarachi da cin amana a aurensu Kungiyar lauyoyi mata ta bayyana damuwarta kan wannan aika-aika, inda ta nemi ‘yan sanda su bi kadin wa danda aka ci zarafinsu Yayin da aka tabbatar da mutuwar daya daga cikin ƴaƴan magidanci, wani rahoto ya nuna cewa matar da sauran ‘ya’yan biyu sun mutu.
An shiga tashin hankali a ƙauyen Onicha Ngwa, karamar hukumar Obingwa, jihar Abia, bayan wani magidanci ya cinna wa kansa da iyalinsa wuta. Ƙungiyar lauyoyi mata ta duniya (FIDA) reshen jihar Abia ta yi Allah-wadai da wannann mummunan lamarin da ya faru da wannan iyali.
An ce magidancin, mai suna Udochi Amala, mai shekara 40, ya cinna wa kansa wuta, da matarsa Amarachi da ‘ya’yansu uku, bisa zargin cin amana daga bangaren matarsa. Rahotanni sun ce Udochi, wanda ke zaune a kauyen Amapuihe, karamar hukumar Osisioma, ya yi ƙoƙarin tserewa bayan faruwar lamarin, sai dai an cafke shi. Wata yarinya daga cikin ‘ya’yansa ta rasu sakamakon ƙonewar da ta yi, kamar yadda rahoton ya nuna.
“Ina da matsala da matata, amma ni kai na ban san cewa matsalar za ta kai wannan matakin ba. Na gaji da rayuwar ne kawai.” Ya kara da cewa bai taɓa kama matarsa, ‘yar asalin ƙaramar hukumar Ikwuano, da wani namiji ba, kawai yana zarginta ne. Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Abia, DSP Maureen Chinaka, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike.
Kungiyar FIDA reshen Abia, ta bayyana matuƙar damuwa da ɓacin rai kan lamarin, tana mai cewa hakan babban cin zarafin ɗan adam ne.
Kungiyar FIDA reshen Abia, ta bayyana matuƙar damuwa da ɓacin rai kan lamarin, tana mai cewa hakan babban cin zarafin ɗan adam ne.