Wani matashi mai shekara 25 ya kashe kansa ta hanyar rataye a jihar Jigawa

0 71

wani matashi dan shekara 25 mai suna Nasiru Badamasi ya kashe kansa ta hanyar rataye a jikin bishiya a garin Tsadawa dake karamar hukumar Taura a Jihar Jigawa.

Hakimin garin na Tsadawa, Alhaji muttaka Uba ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai.

Muntaka Uba ya kara da cewa mutumin wanda yake da aure da kuma ‘ya 1 ya yanke hukuncin kashe kansa bisa dalilin da shi kadai ya sani.

Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta jiha ASP Lawan Shisu Adam shima ya tabbatar da faruwar lamarin.

Shisu Adam ya kara da cewa ‘yan sanda a jiya sun sami rahoton bacewar wani mutum wanda yake fama da cutar tabin hankali tun bayan fitarsa daga gida. Inda daga baya kuma aka samu gawar mutumin bayan ya rataye kansa da wandonsa a wata bishiya.

Yace bayan samun wannan labarin, an tura ‘yan sanda zuwa wajen da abin ya faru an kuma dauki gawar mutumin zuwa babban asibitin Ringim inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: