Wani matashi mai shekaru 28 ya mutu sakamakon zaftarewar kasa a karamar hukumar Taura da ke jihar Jigawa

0 63

Wani matashi mai shekaru 28 mai suna Umar Sale ya mutu sakamakon zaftarewar kasa a karamar hukumar Taura da ke jihar Jigawa.

Kakakin Hukumar Tsaro ta Civil Defence a Jihar Jigawa, Adamu Shehu ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata a garin Majia da ke karamar hukumar Taura a jihar da misalin karfe biyu na rana.

Adamu Shehu ya ce marigayin mai ‘ya’ya uku yana tonon yashi daga rami domin gyara gidansa da ruwan sama mai karfi ya lalata, a lokacin da yashin da ke samansa ya rufto ya binne shi da ransa.

A cewar Adamu Shehu, manoman da ke kewayen yankin sun ji kukan matashin na neman agaji, inda suka garzaya domin ceto shi amma sai gawarsa suka zakulo kuma likitoci sun tabbatar da mutuwarsa.

Ya kara da cewa an mika gawar marigayin ga iyalansa domin yi masa jana’iza.

Leave a Reply

%d bloggers like this: