Wani tsohon mai taimakawa gwamna Muhammad Badaru akan kafafen yada labarai ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ta NNPP

0 102

Tsohon mai taimakawa gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar akan kafafen yada labarai, Bello Zaki, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP.

Tsohon kakakin gwamnan ya sanar da haka a jiya yayin taron zaben shugabannin jam’iyyar NNPP na jihar, da aka gudanar a karamin filin wasa dake Dutse, babban birnin jiha.

Bello Zaki yace ya shiga jam’iyyar tare da magoya bayansa saboda gazawar jam’iyyar APC wajen gudanar da mulki nagari ga ‘yan Najeriya.

Da yake magana a wajen taron jam’iyyar, shugaban kwamitin taron da aka turo daga helkwatar jam’iyyar ta kasa, Takwak Mikaial, yace an kafa jam’iyyar bisa doran turbar demokradiyya.

Yace an samu sabbin shugabannin jam’iyyar na jihar ta hanyar gudanar da sahihin zabe.

Sai dai, ya bayyana cincirindon mutanen da aka gani a wajen taron da ‘yar manuniya cewa akwai alamun nasara kuma mutanen Jigawa sun yi maraba da jam’iyyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: