Wani tsohon shugaban majalisar dattawa ya rasu a wani asibiti a birnin Landan

0 74

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas ya rasu a wani asibiti a birnin Landan.

Har kawo hada wannan rohoton dai ba’asami Cikakkun bayanai game da mutuwarsa ba.

Wayas yana da shekaru 80 a duniya ya shugabanci majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu.

Wayas wanda dan asalin jihar Cross Rivers ne, Gwamna jihar na yanzu Ben Ayade yayi alhinin rashin sa.

Mai taimaka gwamnan kan harkokin yada labarai, Christian Ita ne ya fitar fda wannan sanarwar a madadinsa.

Ayade ya bayyana mutuwar a matsayin wani babban rashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: