Wani Yaro Ya Nutse A Cikin Wani Tafki A Kauyen Makugara Da Ke Karamar Hukumar Karaye A Jihar Kano

0 175

Wani yaro dan shekara 13 mai suna Yusuf Magaji ya nutse a cikin wani tafki da ke kauyen Makugara da ke karamar hukumar Karaye a jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce yaron tare da takwarorinsa daliban makarantar Malam Nafiu Na Adama Tsangaya suna wanki a tafkin sai ya zame ya fada ciki.

Kakakin hukumar kashe gobara, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce ofishinsu da ke Karaye ya samu kiran gaggawa daga Malam Nafi’u Na Adama wanda ya kai rahoton faruwar lamarin a kauyen Makugara da ke karamar hukumar Karaye.

A cewarsa, an ce daliban suna kan hanyarsu ta zuwa wani kauye ne a lokacin da suka tsaya kusa da kuddufin domin yin wanka.

Ya kara da cewa mutanen su na Karaye sun yi nasarar dauko wanda ya nuste a sume kuma suka kai shi asibitin kwararru na Karaye domin kula da lafiyarsa, inda daga bisani likita ya tabbatar da rasuwarsa. Sai dai Abdullahi ya ce an mika mamacin ga Malam Nafi’u Na Adama, mai kula da Makarantar Tsangaya.

Leave a Reply