Wasiƙar Obasanjo Na Iya Haddasa Tashin Hankali A Ƙasar Nan – Tanko Yakasai

0 303

Fitaccen ɗan siyasar nan kuma guda daga cikin manyan dattawan Arewa wadanda suka kafa Kungiyar nan ta hadin kan al’ummar yankin Arewa (Consultatibe Forum), Alhaji Tanko Yakasai, ya yi martini akan wasikar da tsohon shugaban ƙasar nan, Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Tanko Yakasai ya bayyana cewa ire-iren waɗannan wasiƙu da tsohon shugaban ƙasar ya saba fitarwa da ma can ɗabi’arsa ce ta rashin kishin ƙasa tare da son zaman lafiya.

Ya ƙara da cewa wannan wasiƙar da Obasanjo ya rubutawa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, na iya haddasa mummunan tashin hankali a ƙasar nan musamman idan aka yi la’akari da abubuwan da ke kunshe da ita.

“Ko shakka babu son kai ne da rashin kishin ƙasa ke sanya Obasanjo yin irin wannan rubutun. Domin haka, aikin da tsohon shugaban ƙasa ya ke yi, ba komai ba ne illa ƙoƙarin haddasa fitina ko tashin hankali a wannan ƙasa, idan har ire-iren waɗannan kalamai ko sakwanni na ƙiyayya za su ci gaba da yaduwa a cikin al’umma,”

Haka zalika, irin wannan rubutun wasika ne ya jawo wa Obasanjon shiga gidan yari a lokacin mulkin Janar Sani Abacha.

“Kazalika na fahimci cewa, manya-manyan sojojin ƙasar nan a kullum ta Allah cikin fada suke da junansu, koda kuwa bayan sun yi ritaya. Domin haka, ba wannan ne karo na farko ko na biyu ba, a wajen Obasanjo”

Domin kuwa Obasanjo ya yi irin wannan a lokacin Shugaban Kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, Janar Abdussalami Abubakar, da kuma Goodluck Jonathan, har zuwa kan Muhammadu Buhari, inda wanda kuma babu wani abin kirki a cikin abin da Obasanjon ya ke rubutawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: