Wasu fusatattun mutane sun dauki doka a hannu kan barawo a karamar hukumar Gwaram

0 94

Wasu fusatattun mutane sun dauki doka a hannu kan wanda ake zargi barawon babur ne a karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya ce lamarin ya faru ne jiya a Kauyen Kila da ke karamar Hukumar Gwaram.

Ya bayyana cewa ‘yan sanda a Gwaram sun samu labarin cewa wasu fusatattun matasa sun cafke wani da ake zargi barawon babur ne, inda suka yi masa duka suka bar shi cikin jini.

Shiisu Adam ya ce ‘yan sanda sun garzaya wurin da abin ya faru kuma sun gano cewa wanda ake zargin ya sha mugun duka a hannun jama’a.

Ya ce an kubutar da wanda abin ya rutsa da shi kuma an garzaya da shi zuwa karamin asibitin Gwaram don yi masa magani sannan daga bisani likita ya tabbatar da mutuwarsa yayin da yake karbar magani.

Kakakin ‘yan sandan ya ce an gayyaci wasu ‘yan banga biyu da ake zargi da hannu a kisan don amsa tambayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: