Labarai

Wasu maniyyata aikin Hajji bana sunyi zanga-zanga a kofar gidan gwamnatin jihar Lagos biyo bayan kara kaso 100 na kudin aikin Hajjin 2022

Wasu Maniyyata aikin Hajji Bana a Jihar Lagos sun gudanar da zanga-zanga a kofar gidan Gwamnatin Jihar da ke Alausa, biyo bayan kara kaso 100 na kudin aikin Hajjin na shekarar 2022.

Maniyatan sun ce sun riga sun biya kudin aikin Hajjin 2020 tun cikin shekarar 2019, amma basu je ba saboda cutar Corona.

A cewarsa, sai suka samu sakon waya daga hukumar aikin Hajji cewa zasu kara biyan Naira Miliyan 1 da Dubu 300 domin cike gibin karin kudin da aka samu, bayan sun riga sun biya a 2019.

Daya daga cikin Maniyata aikin Hajjin wanda ya yi magana a madadin sauran Maniyata na kananan hukumomin Jihar ya ce tun da farko sun biya Naira Miliyan 1 da dubu 300 a shekarar 2019, amma abin mamaki sai suka samu sako daga hukumar kyautata walwalar Maniyata aikin Hajji cewa kudin ya sake karuwa, inda ake bukatar su sake biyan Naira Miliyan 1 da dubu 340 cikin kwanaki 5, ta yadda zai zama Naira Miliyan 2 da dubu 640 kenan.

Hakan na nufin ga Maniyata kudin aikin Hajjin bana zai zama Naira Miliyan 2 da dubu 640 kenan.

Masu zanga-zangar sun bukaci Gwamnan Jihar Babajide Sanwo-Olu da Kakakin Majalisar Dokokin JIhar Mudashiru Obasa, su shiga lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: