Wasu Matasa Sun Kashe Mutum Guda Da Kone Gidaje 64 Da Babura 3 Tare Da Lalata Kadarori Na Miliyoyin Naira A Bauchi

0 198

Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi tace wasu fusatattun matasa sun kashe mutum guda da kone gidaje 64 da babura 3 tare da lalata kadarori na miliyoyin naira a yankin karamar hukumar Bogoro ta jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Ahmed Wakili, ya rabawa kamfanin dillancin labarai na kasa a Bauchi.

Yace hakan ya auku ne sanadiyyar wata zanga-zanga da fusatattun matasa suka gudanar akan nadin dagacin kauyen Sanga a karamar hukumar.

Ya kara da cewa an kashe mutum guda a lamarin yayin da wasu mutane suka jikkata a rikicin.

Kakakin yace jami’an ‘yansanda sun dawo da zaman lafiya cikin gaggawa bayan amsa kiran daukin gaggawa kuma kokarinsu ya haifar da zaman lumana.

A cewarsa, kwamishinan ‘yansandan jihar, Aminu Alhassan, ya umarci DPO na Bogoro da ya kaddamar da binciken sirri domin bankado lamuran da suka jawo hatsaniyar.

Leave a Reply