Wasu mutane sun kashe wata mai zaman kanta mai shekaru 35 Hadejia cikin jihar Jigawa

0 52

Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kashe wata mata mai zaman kanta mai shekaru 35 mai suna Ladi Anndu a Hadejia, jihar Jigawa.

Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa an gano matar ne a dakinta da ke unguwar Gandun Sarki kwance cikin jinin.

Ya ce wadanda suka kashe ta, wadanda ake zargin abokan huldarta ne, sun yi amfani da wuka wajen yanka mata makogwaro.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jiha, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a jiya.

A cewar sa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar.

Ya ce bayan da ‘yan sanda suka samu rahoton, tawagar ‘yan sandan ta garzaya wurin da lamarin ya faru, inda aka kai matar zuwa asibiti domin ceto rayuwarta cikin gaggawa.

Shiisu ya kara da cewa, matar ta mutu ne a lokacin da ake kokarinta ceton ta kuma likita ne ya tabbatar da mutuwarta.

Ya ce an gano almakashi da tabon jini a wurin a matsayin shaida, inda ya kara da cewa ana gudanar da bincike kan lamarin yayin da ake kokarin cafke wadanda ake zargin sun kashe ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: