Wasu mutum 12 sun mutu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Ilorin zuwa Ogbomoso

0 32

Akalla mutane 12 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Ilorin zuwa Ogbomoso.

Hadarin ya afku ne da safiyar jiya a hanyar Ote express inda wasu mutane 6 kuma suka samu raunuka.

Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa ce ta, tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce hatsarin ya faru ne saboda cin zarafin hanyoyin mota, da keta haddi, da kin kiyaye ka’idojin bin shtale-tale da kuma rashin tsaro.

Kwamandan sashin ya ce hatsarin ya rutsa ne da wata farar mota kirar Toyota Hummer wacce ba ta da lambar rajista da wata farar tirela Volvo wacce ita ma ba ta da lambar rajista.

Ya kuma kara da cewa an kai wadanda suka jikkatan da kuma gawarwakin zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin

Leave a Reply

%d bloggers like this: