Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne sun yi garkuwa da wani limamin Cocin Saint Patrick, Stephen Ojapa da mataimakinsa Oliver Okpara a kauyen Gidan Mai Kanbu da ke karamar hukumar Kafur a jihar Katsina.

Majiyoyin cikin gida sun bayyana cewa da sanyin safiyar yau ne ‘yan bindigar suka kai farmaki harabar cocin inda suka tafi da su tare da wasu mutane biyu da ake kyautata zaton bakinsu ne.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ’yan bindigar da ake zargin sun zo ne a kan babura, amma suka ajiye su a wani wuri mai nisa, sun yi tattaki zuwa harabar cocin.

A wani labarin kuma, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai farmaki kauyen Bare-Bari da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da mutane hudu.

Wani mazaunin garin ya ce wani shahararren dan siyasa a kauyen, Alhaji Dan Mashubulle yana cikin wadanda aka sace yayin harin.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isa, ya ce rundunar ba ta da masaniyar satar mutanen.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: