Wasu ‘yan bindiga sun harbe daya tare da sakin da wasu manoma 12 da suka yi garkuwa da su a kauyukan Kutunku da Gasakpa dake unguwar Gurdi a karamar hukumar Abaji a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotan City & Crime majiyar ya bayyana cewa ‘yan bindigar a ranar Asabar data gabata sun kashe wani manoni, tare da sace wasu 13.

Dan uwan daya daga cikin manoman da aka sallamo Shuaibu Ibrahim ya ce, sun tara naira miliyan 8 da buhunan shinkafa da giya da kuma kwayoyi kafin su sako 12 daga cikinsu, amma daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya mutu.

Ya ce an sako mutanen da aka sace jiya da yamma a wani daji da ke jihar Neja wanda ke kan iyaka da babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce an kai gawar wanda aka kashe zuwa gida kuma tuni akai masa jana’iza.

Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Adeh Josephine, bai amsa sakon kartakwanan da manema labarai suka aike masa ba game da faruwar lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: