Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wata coci da ke jihar Ogun inda suka yi awon gaba da wasu masu ibada guda biyu

0 83

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki wata coci da ke karamar hukumar Ewekoro a jihar Ogun, inda suka yi awon gaba da wasu masu ibada guda biyu.

An rawaito cewa ‘yan ta’addan sun kai farmaki cocin ne da misalin karfe 11 na daren jiya inda suka tafi da masu ibadan biyu.

An kuma rawaito cewa rundunar hadin guiwar jami’an tsaro ta ‘yan sanda da ’yan banga sun yi ta karade dazuka a yankin domin neman wadanda aka sace.

Shugaban cocin ya tabbatar da faruwar lamarin a yau.

Ya kuma tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun isa cocin inda suka nemi kudin fansa na naira miliyan 50.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce ba a yi masa bayani dangane da lamarin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: