Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane da dama a sallar asuba a wani masallaci a jihar Neja

0 53

Rundunar ‘yan sanda a jihar Neja ta ce wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba da ke sallar asuba a wani masallaci da ke kauyen Mazakuka da ke karamar hukumar Mashegu a jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Kuryas, wanda ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran na Kasa, jiya a Minna, ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu masallata su bakwai a masallacin.

Monday Kuryas ya ce lamarin ya faru ne a jiya da misalin karfe 5 da rabi na asuba, lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari kauyen.

Ya ce daga baya ‘yan bindigar sun lalata kadarori na miliyoyin naira mallakin wani mai suna Abubakar Maigandus a kauyen.

Ya ce jami’an tsaro, sun harbe daya daga cikin ‘yan fashin dajin.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce an gano lamarin a matsayin harin ramuwar gayya, da ya samo asali daga rikicin kabilanci da aka dade ana yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: