Wasu yan bindiga sun saki fursunoni a babban gidan yarin da ke Jihar Oyo biyo bayan wani hari da suka kai da tsakar dare.

Mazauna garin Oyo sun shaida mana cewa maharan sun yi amfani da ne abun fashewa ne wajen balla babbar kofar shiga gidan yarin da misalin karfe 10 na dare ranar Juma’a.

Shaidu sun ce ganin hakan ne ya sa jami’an tsaron da ke cibiyar neman mafaka domin tsira da rayuwarsu.

Manema Labarai sun gano cewa maharan sun saki daukacin fursunonin da suke gidan yarin.

Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Yari na Jihar Oyo, Mista Lanre Anjorin, ya tabbatar da kaiwa harin.

A cewarsa’ Kwanturolan Hukumar Kula da Gidajen Yari da manyan jami’an hukumar suna tantance abin da ya faru.

Matsalar tsaro dai ta dabaibaye sassan Najeriya, lamarin da Gwamnatin Tarayya ta ke ta kokarin shawon kansa.

Kawo yanzu dai babu tabbacin wanda ya kai harin, sai dai ya yi alakawarin bayar da cikakken bayanai kan harin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: