Wasu yan kungiyar ISWAP ne sun kashe ‘yansanda 2 da wani soja guda a jihar Borno

0 81

Wasu daga ake zargin yan kungiyar ISWAP ne sun kashe ‘yansanda 2 da wani soja guda a Malam Fatori, helkwatar karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun tabbatar da hakan ga manema labarai, inda suka ce wadanda aka kashe ‘yan wani kwamitin tsaro ne dake sumame a yankin, a shirye-shiryen dawowar ‘yan gudun hijira.

Gwamnatin jihar Borno a halin yanzu tana shirin rufe sansanonin ‘yan gudun hijira.

Wata majiyar tsaro tace dakarun wadanda aka aika domin aiki, sun gamu da farmaki kuma suka mayar da martanin gaggawa.

Kungiyar ISWAP ta sabunta hare-harenta a yankin Arewa masu Gabas tun bayan kisan shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, da shugaban ISWAP, Musab Al Barnawi.

An bayar da labarin yadda mayakan suka cinna wuta kan wani asibiti a jihar Borno tare da kone wani karfen sadarwa.

A ‘yan kwanakinnan, kungiyar ta saki wani faifan bidiyo dake nuna yadda daya daga cikin mayakanta ya kashe wasu sojoji da aka kama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: