Wata abbar kotun jihar Kaduna ta umurci wata jarida da ta biya gwamna El-Rufai naira miliyan 10 a matsayin diyya

0 122

Wata abbar kotun jihar Kaduna ta umurci wata jarida da ta biya gwamna Nasir El-Rufai naira miliyan 10 a matsayin diyya, tare da neman gafarar jama’a kan wani labari da ta wallafa cewa gwamnan ya bayyana kadarorinsa na naira biliyan 90.

Kotun ta bayar da umarnin ne a jiya a wani hukunci da mai shari’a M.L. Muhammed ya yanke, a karar da El-Rufai ya kai kan Kamfanin Jarida na Today.

Kotun ta ce dole ne a buga neman gafara a jaridun kasarnan, sannan kuma ta hana wadanda ake tuhuma ci gaba da bata sunan gwamnan.

Jaridar a ranar 2 ga watan Yulin 2015 ta yi ikirarin cewa gwamna El-Rufai ya bayyana mallakar naira biliyan 90, ciki har da gidaje 40, a cikin fom din daya bayyana kadarorinsa.

El-Rufai ya bayyana labarin a matsayin kanzon kurege kuma na zalunci, inda daga bisani ya shigar da karar jaridar a gaban kotu.

A hukuncin da kotun ta yanke, El-Rufai ya tabbatar da hujjojin da ya bayar cewa bai taba bayyana kadarorin da ya kai Naira biliyan 90 da kuma gidaje 40 ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: