Labarai

Wata babbar kotun jihar Jigawa ta zartar da hukuncin daurin rai da rai ga wani mutum a karamar hukumar Birnin Kudu bisa laifin aikata fyade

Wata babbar kotun jiha dake zamanta a Birnin Kudu ta zartar da hukuncin daurin rai da rai ga wani mai suna Isa Ibrahim Kwari dake kauyen Kwari na karamar hukumar Birnin Kudu bisa laifin aikata fyade.

Da yake zartar da hukuncin, Alkalin kotun Mai shari’a Musa Ubale ya bayyana cewa kotun ta samu wadda ake kara da laifin yiwa yarinya ‘yar shekara hudu fyade a gonar sa a wani lokaci cikin shekara ta 2018.

Kotun ta gamsu da shedun da lauya mai gabatar da kara ya gabatar mata, inda ta tabbar da wanda ake kara da aikata laifin, don haka kotun ta zartar masa da hukuncin daurin rai da rai karkashin sashi na uku na kundin laifuka na Penal Code na jihar Jigawa wanda aka yiwa gyara a shekara ta 2014.

Daraktan sashin ayyuka na musamman da harkokin baki na hukumar shari’a ta jihar Jigawa, Abbas Rufa’i Wangara, ya ce kotun ta zartar da hukuncin ne a zaman data yi a garin Birnin Kudu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: