Wata hatsaniya ce ta bulla a garin Yauri na jihar Kebbi dake Arewacin Najeriya tsakanin ‘yan sa kai da Fulani abin da yayi sanadiyar mutuwar mutum uku wasu suka samu raunuka.
Yanzu haka jama’ar garin na zaman dar-dar saboda rashin sanin abinda zai iya sake faruwa sanadiyar wannan yamutsin wanda mutanen garin basu saba ganin irinsa ba.
Rigimar ta soma ranar Asabar dake zama ranar kasuwar garin na Yauri inda wasu ‘yan sa kai da ke farautar barayin shanu suka zo sashen turaku inda ake sayar da dabbobi suna neman kama wani bafulatani da suke tuhuma.
Zuwan su wurin ke da wuya suka yi yunkurin kama mutumin sai ‘yan uwansa suka hana, suka bukaci a tsaya ayi binciken tuhumar da ake masa kafin kama shi inda nan ne rigima ta barke har aka soma sare-sare abinda ya tayar da hankalin jama’a suka shiga gudu.
Da aka zanta da wani mazaunin garin Shamsu Yauri ya shedi aukuwar lamarin wanda ya sa jama’a gudu don neman tsira.
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi ta bakin kakakinta DSP Nafi’u Abubakar ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Asabar.
Yankin na Yauri dai a iya cewa shine na biyu da ya fara fuskantar rigima tsakanin Fulani da ‘yan sa kai har akai ga yin kisa baya ga yankin Zuru da aka yi ta samun irin wadannan matsalolin.
Rundunar ‘yan sanda jihar ta ce ta kaddamar da wani shiri na Operation GANUWA domin magance shigowar ‘yan ta’adda daga wasu wurare suna addabar jama’ar Kebbi.