Wata kotu a birnin Dutse ta zartar da hukuncin daurin shekaru 28 da watanni 5 akan wasu mutane uku bisa lefin sata da aikata ta’addaci

0 82

Wata Babbar kotun jiha dake zamanta a Dutse babban birnin jiha ta zartar da hukuncin daurin shekaru 28 da watanni biyar akan wasu mutane uku bisa lefin sata da hadin baki da kuma aikata ta’addacin.

Mutanen masu suna Musa Garba dake kauyen Jiyau na Karamar Hakumar Ringim, da Isa Sule dake kauyen Wangara a Karamar Hakumar Dutse da kuma Shu’aibu Haruna dake Shangel a Karamar Hakumar Ringim, an same su da lefin aikata fyade da kuma sace wata Mata mai suna Fatima Abdulrahman dake garin Taura.

Mai gabatar da kara ya gabatar da shedu hudu tare da gabatar da shedar aikata lefukan wanda hakan ya sabawa sashe na 272 da sashe na 273 na dokar panel code.

Leave a Reply

%d bloggers like this: