Wata kotu a Hadejia ta yankewa wani mutum hukuncin zama a gidan gyaran hali saboda kamashi da yin fashi da makami

0 68

Wata Babbar Kotu dake Zaman ta a nan Hadejia a jiya ta yankewa Malam Ali Idi hukuncin daurin shekaru 7 a gidan gyaran hallaya biyo bayan kama shi da laifin fashi da makami a karamar hukumar Kirikasamma.

Da yake yanke hukunci Alkalin Kotun Mai Sharia Ado Yusuf Birnin Kudu, ya ce kotun da kama mutumin da laifukan cin amana da kuma fashi da makami.

A cewarsa, mutumin ya aikata laifin ne a ranar 30th ga watan Yuli na shekarar 2018, a karamar hukumar Kirikasamma inda suka hada kai da wani wanda har yanzu ake neman mai suna Gando, wajen yin fashi a shagon Bala Muhammad, ta hanyar yin amfani da adda da kuma kuma wukake, inda suka sace abinci masu tarin yawa.

Mai Sharia’a Ado Yusuf ya ce laifin ya sabawa sashe na 97 da na 298 (b) na kundin Penal Code ta Jihar Jigawa.

Haka kuma ya ce mutumin ya amsa laifin sa, bayan kamashi da laifukan da ake zargin sa dasu.

Kazalika, ya ce an yanke masa hukuncin ne saboda cin amana da kuma fashi da makami.

Leave a Reply

%d bloggers like this: