Wata kotu a Amurka ta sami wani uba da dansa da laifin kashe wani bakar fata yayin da yake gudun motsa jiki.

Kotun ta sami Travis da dansa Gregory McMichael da wani makwabcinsu William Bryan da laifin kashe Ahmaud Arbery saboda kawai shi bakar fata ne a watan Fabrairun 2020.

Dukkan mutanen, wadanda turawa ne za su shafe sauran kwanakin da suka rage mu su a gidan kurkuku, sai dai mutum na uku na iya neman a sako shi bayan shekaru talatin

Yayin da yake yanke musu hukunci, alkalin kotun ya ce turawan uku sun katse rayuwar wani dan Adam din da ba su da damar katsewa, kuma ya koka kan irin rashin imanin da mutum biyu na farko – wato Gregory da dansa suka nuna wa Ahmaud Arbery.

A karkashin dokar jihar Georgia, daurin rai-da-rai ne hukunci mafi kankanta da alkalin zai iya yanke wa wadannan turawan uku.

Ya yi wa mahaifi Gregory mai shekara 66 da dansa Travis mai shekara 35 daurin da za su shafe sauran kwanakinsu a daure a cikin kurkuku, inda mutum na uku kuwa sai bayan shekara 30 za a duba batunsa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: