Wata kotu ta yanke hukuncin tura wani fitaccen ɗan gwagwarmaya gidan kaso bayan ta same shi da laifin yaɗa labaran ƙarya

0 118

Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar a gidan kaso ga wani fitaccen dan gwagwarmaya Alaa Abdel Fattah bayan ta same shi da laifin yada labaran karya.

‘Yar uwarsa Mona Seif ta bayyana hakan a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, inda ta kara da cewa an kuma daure lauyan kare hakkin bil’adama Mohammed al-Baqer da mawallafi Mohammed Ibrahim a gidan yari na tsawon shekaru hudu bisa laifin.

An tsare mutanen biyu tun watan Satumban 2019, lokacin da jami’an suka murkushe zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: